News
Dukkan ‘yan Boko Haram din da ke daure a Kuje sun tsere — Minista
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Ministan harkokin tsaro a Nigeria, Bashir Salihi Magashi, yayin jawabi ga manema labarai kan harin Kuje, ya ce mambobin kungiyar Boko Haram 64 ne suka tsere daga Gidan Yarin bayan kai harin.
Magashi yace a halin yanzun komai ya koma ƙarƙashin kulawa yayin da dakarun soji suka mamaye wurin kuma iko ya koma hannun su.
“Muna iya bakin kokarin mu wajen ganin duk wanda ya tsere bai sha ba, mun dawo da su inda suke.”
Jaridar Legit.ng ta rawaito cewa, Ministan ya ce jami’an tsaron da ke cikin harabar gidan Yarin sun yi kokarin maida martani iya karfin su amma yan ta’addan sun zo da adadi mai yawa na mayaƙa.
“Daga kididdigar da muka yi, suna da alaƙa da wata kungiya wato ƙungiyar ta’addancin Boko Haram, baki ɗaya mambobin su da ke ciki sun tsere.”
“Amma yanzu komai ya dai-daita, shiyasa zaku ga mutane sun cigaba da harkokin su na yau da kullum. Mun nemi karin ɗauki kuma sojoji sun zo, sun karɓi ikon komai.” — inji shi
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
