Majalisar Dokokin Tarayya ta mayar wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kasafin kudin kasar na shekarar 2022 domin ya sanya masa hannu.
Akawun Majalisar Dokokin, Amos Ojo, ne ya aike wa shugaban kasar kasafin kudin tare da wasikar da aka rubuta ranar 24 ga watan Disamba, a cewar jaridar Premium Times da ake wallafawa a shafin intanet.
Ta kara da cewa Akawun Majalisar Dokokin ya shaida wa Shugaba Buhari cewa ya aike masa da kasafin kudin ne kamar yadda dokokin Najeriya suka bukaci ya yi.
Ya aike da kasafin kudin ne mako guda bayan ‘yan majalisar dattawa da na wakilai sun amince da shi.
‘Yan majalisar sun amince da naira tiriliyan 17.1 maimakon naira tiriliyan 16.3 da shugaban ya nemi su amince – abin da ke nuna sun kara naira biliyan 700.
Dokokin Najeriya sun bai wa ‘yan majalisar damar karawa ko rage adadin kasafin