News
‘Ƴan bindiga sun sace fasinjoji daga motoci goma a Zamfara’
A daidai lokacin da aka shiga sabuwar shekarar ta 2022 miladiya, ‘yan bindiga a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da kai farmaki ga al’umma a kan hanyoyin mota da ke cikin jihar.
A cikin wani hari da suka kai da dare zuwa safiyar jiya Asabar kan motocin sufuri, ‘yan bindigan sun kwashi jama’a da dama tare da halaka wasu.
Wata mata da ta auna shekara da ke cikin daya daga cikin motocin da ta rasa abokiyar tafiyarta, ta yi wa BBC karin bayani kamar haka:
“Mun taso daga garin Jibiya da karfe huɗu kuma mun isa Funtua da misalin ƙarfe bakwai da wani abu. Daga nan mun wuto ‘Yankara zuwa garin Kuceri. Ba mu san da su ba saboda suna cikin duhu ne. Kawai sai muka ji ƙarar harbi a ko’ina.”