News
Jami’ar Anambra ta bada tallafi ga tubabbun karuwai da masu ƙaramin ƙarfi 5,000
Daga kabiru basiru fulatan
Jami’ar Anambra ta bada tallafi ga tubabbun karuwai da masu ƙaramin ƙarfi 5,000
Jami’ar Tansian, Umunya, Jihar Anambra da haɗin gwiwar wata cibiyar ci gaban ilimi ta Britaniya, CIEPUK, ta bada cikakken tallafi 5,000 ga tubabbun karuwai da masu ƙaramin ƙarfi.
Shugaban CIEPUK na ƙasa, Marcel Ezenwoye ne ya baiyana haka ga manema labarai a Abuja a yau Talata.
Ezenwoye ya ce an zaɓo waɗanda su ka amfana da tallafin da ga jahohi 36 na ƙasa har da Abuja.
“Jami’ar Tansian, Umunya, Jihar Anambra da haɗin gwiwar wata cibiyar ci gaban ilimi ta Britaniya, CIEPUK, ta bada cikakken tallafi karatu 5,000 ga tubabbun karuwai da masu ƙaramin ƙarfi da ga kowacce jiha cikin jihohi 36 na ƙasar nan gami da Abuja.
“Waɗanda za su amfana da tallafin sun zo ne bayan da kowacce gwamnatin jiha ta aika bayanan ko wacce mace da ta amfana.
“Za a yi musu horo ma watanni uku a kan sana’o’in hannu daban-daban sannan a basu kayaiyakin aiki bayan sun kammala.
“Da ga 26 ga watan Febrairu, waɗanda su ka amfana za su halarci horon ne a ɗaya da ga cikin cibiyoyi biyu na yankin Arewa da na Kudu kuma za su tafi ne a tsarin rukuni-rukuni.
“A horon na watanni uku za a koya musu ƙera takalmi, yadda a ke sabulu da man shafawa, rubuce-rubuce, haɗa fefen bidiyo da noma.
“Sauran sun hada da zama jarumar wasan kwaikwayo, Ilimin kafafen sadarwa, harkar haɗa fim, haɗa kayan gado, gyaran wuta, aski, haɗa kayan yaji da kuma harkar haɗa gurin tarurruka da sauransu,”
Shugaban ya baiyana cewa a rukunin farko na aikin, mutane dubu 185,000 za a yaye.