Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Neves, Coutinho, Origi, Williams, Phillips, Digne, Gomez da Haaland

Published

on

122598489 76c91747 dd5d 4f6c 8bd1 843544a4248c.jpg
Spread the love

 Daga Usman Abdullahi Nguru

Manchester United na da kwarin gwuiwar sayen dan wasan tsakiyar Wolves da Portugal Ruben Neves a wannan watan na Janairu. (The Sun)

Kocin Aston Villa Steven Gerrard ya kira Philippe Coutinho na Barcelona wanda da dama suka buga tare a Liverpool, da ya amsa bukatarsa ta zuwa Villa buga masa wasa. (El Partidazo de Cope, via Mirror)

Advertisement

Lazio ta Italiya kuwa ta fara tattaunawa da Liverpool kan duba yiwuwar daukar Divock Origi da kwantiraginsa ke karewa a karshen kaka. (LazioNews24 – in Italian)

Hakama (Sky Sports) ta ce Liverpool na za ta iya sakin masu tsaron baya Neco Williams da Nathaniel Phillips a wannan wata na Janairu.

Dan wasan tsakiyar Wales Aaron Ramsey zai bar Juventus, inda yanzu haka yake karbar fam 325,000 a duk mako. (Sky Sports)

Watakila mai tsaron baya Lucas Digne ya bar Everton zuwa Newcastle. (Fabrizio Romano via Twitter)

Advertisement

Anan kuma Everton din da Newcastle har ma da Arsenal na rige-rigen daukar dan wasan tsakiyar Lyon da Brazil Bruno Gimaraes. (Evening Standard)

Chelsea na duba yiwuwar daukar mai tsaron bayan Barcelona Sergio Dest idan har ba ta samu Digne ba. (Daily Star)

Barcelona ta taya wa Newcastle mai tsaron bayanta Samuel Umtiti. (Daily Mail)

Advertisement

Ita kuma Aston Villa ta hakura da sayen mai tsaron bayan Liverpool Joe Gomez. (Athletic – subscription required)

Borussia Dortmund za ta yanke hukunci kan makomar Erling Haaland nan da makonni masu zuwa. (Daily Mail)

A nan kuma West Ham ta zube fam miliyan biyar, don karbar aron dan wasan gaban Flamengo na Brazil Gabriel Barbobosa. (Sport – in Spanish) .

Advertisement

Kusan ‘yan wasa 11 ne suka gaji da zama a Manchester United, yayin da ake ta jita-jitar cewa ana samun rashin jituwa a dakin sauya kaya. (Mirror)

A wata mai kama da haka Manchester United na kokarin sayen mai tsaron bayan Borussia Dortmund Dan-axel Zagadou. (Foot Mercato – in French)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *