Connect with us

News

Mutuwar Dr. Ahmad babban giɓi ne a duniyar ilimin Hadisi – Atiku

Published

on

1FE4F716 CA86 460F 99D7 8DA9F283C0B3 w408 r1
Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

 

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar babban malamin addinin nan na Kano, Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, wanda a ka fi sani da Kala Haddasana wanda ya rasu a jiya Juma’a.

Atiku wanda ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a ya ce, ya yi matuƙar kaduwa lokacin da ya samu labarin rasuwar Dr. Ahmad.

Advertisement

“Na kaɗu matuƙa da samun labarin rasuwar Dr. Ahmad Ibrahim Bamba”.

“Rasuwar Shehin Malamin ya bar babban giɓi a duniyar ilimin Hadisi wanda zai yi wahalar cikewa.

“Mutuwar sa babban rashi ne ga duniyar Ilimin Hadith da sauran rassan Ilman Musulunci. Ya sadaukar da dukkan rayuwarsa wajen ilmantarwa da wayar da kan mutane. Haƙiƙa an saurari karatuttukansa a dukkan sassan duniya”.

Advertisement

“Ina addu’ar Allah ya ji ƙan sa sannan ya bai wa iyalai da abokansa haƙurin rashinsa. “Addu’ar Allah ya gafarta masa zunubansa, Ya haɗa shi da salihan bayi, ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus. Ameen”. In ji Atiku

Sheikh Dr. Ahmad ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano kamar yarda PlatinumPost ta ruwaito.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *