Connect with us

Business

Ƙungiyar tagwaye ta yi zaɓen shugabanni a Kano

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Kungiyar Inuwar Tagwaye ta Ƙasa, reshen Jihar Kano ta gudanar da zaɓen shugabaninta karo na farko, domin sake fasalin shugabancin ƙungiyar don inganta harkokin ta.

Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen, Hassan Isah Muhammad Gwale shi ne ya jagoranci zaɓen.

Da ya ke jawabi bayan kammala zaɓen, Gwale ya sanar da Engineer Hassan Ahamad Makeri a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar, sai Kuma Hassan Auwal Muhammad, wanda a ke kira da Jack City ya zama mataimakin shugaba.

Advertisement

Ya kuma sanar da cewa an zaɓi Hussaini Kabir Minjibir a matsayin sakataren Ƙungiyar.

A jawabin nasa, Gwale ya buƙaci waɗanda su ka samu nasara da su yi aiki tukuru domin ciyar da ƙungiyar gaba.

Ya kuma buƙaci wadanda basu samu Nasara a zaben ba, da su marawa wadanda su ka samu nasarar baya domin ciyar da kungiyar gaba.

Advertisement

An dai gudanar da zaben ne a makarantar gidan makama da ke Kano, inda tagwaye mata da maza daga ƙananan hukumomi arba’in da huɗu na jihar su ka halarci zaɓen.

Sabbin Shugabannin dai a na sa ran za su tafiyar da harkokin Kungiyar dai-dai da yadda kundin tsarin Mulkin Kungiyar ya gindawa ba tare da son rai ba.

A Jawabinsa bayan rantsuwar kama aiki sabon Shugaban Ƙungiyar Tagwayen, Engineer Hassan Ahmad Makeri, wanda ya yi magana a madadin Sauran Shugabannin, ya bada tabbacin za su yi aiki tuƙuru tare da bujiro da sabbin dabarun da za su ciyar da Ƙungiyar gaba.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *