News
Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban hukumar yaki da safara da ta’amuni da muggan kwayoyi NDLEA, Buba Marwa, ya ce babu unguwar da ta tsira daga matsalar yan kwaya a Najeriya.
Marwa ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da shugabannin kananan hukumomin jihar Plateau, rahoton TheCable.
Tsohon Sojan yace kimanin yan Najeriya milyan 15 ke ta’amuni da haramtattun kwayoyi.
A cewarsa, wannan abu na bada gudunmuwa wajen tsanantar matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.
Yace: “Yanzu haka da nike magana, yan Najeriya milyan 15 ke ta’amuni da kwayoyi; kowani mutum daya cikin mutane bakwai na shan muggan kwayoyi.”
“Babu unguwar da ta tsira a Najeriya daga kwaya, shiyasa muke fama da matsalolin tsaro ko ina.”
“Shi yasa muke kira ga shugabannin kananan hukumomi su bamu hadin kai wajen kawar da matsalar kwaya a cikinmu.”