Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta ce ci gaba da jinkiri wajen amincewa da dokar zabe ta (2010) da Majalisar Dokokin ƙasar ta yi na iya yin tasiri kan amincewa da sabbin gyare-gyare a babban zaben 2023.
Hukumar ta ce duk da cewa tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin dokokin da ake da su, amma yana da muhimmanci a samar da dokar da za ta jagoranci gudanar da zaben akalla watanni 12 zuwa 18 kafin gudanar da zaben.
Tuni dai Shugaban Hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana ranar 23 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa, wato nan da shekara daya kenan.
Gyaran dokar zaben dai ya haifar da zazzafar muhawara a Najeriya musamman kan bukatar watsa sakamakon zaben ta Internet, da kuma zaɓen yar tinƙe ga kowacce jam’iyya.