News
Ƴan bindiga sun sace mutane 15 a Jihar Naija
Daga kabiru basiru fulatan
Rundunar ƴan sandan Najeriya, reshen Jihar Naija ta tabbatar da sace mutum 15 a ƙauyen Kulho da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu.
Jaridar Premium Times ta ruwaito mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin.
Abiodun ya baiyana cewa da misalin ƙarfe 2 na dare ne a ranar 14 ga watan Janairu, wasu da ake zargin ƴan bindiga ne su ka afka ƙauyen inda su ka sace shanu ba iyaka.
Ya baiyana cewa an tura dakarun ƴan sanda domin su ceto waɗanda a ka sace.
Jihar Naija na da ga cikin jihohin Nijeriya da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
A jiya Lahadi ne dai Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa sojoji umarnin anfani da karfi su murƙushe ƴan ta’adda masu garkuwa da mutane da kashe-kashe a Jihar ta Naija.
Mai taimakawa Shugaban Ƙasa ta Bangaren Kafafen Yaɗa Labarai, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaban ƙasar ya bada umarnin ne ga Shalkwatar Sojoji ta ƙasa.
Ya ce Buhari, a matsayin sa na Babban Kwamandan Tsaro a ƙasa, ya bada umarnin sojoji su fara fatattaka ƴan ta’addan a Naija, jihar da ke fama da ayyukan ƴan fashin daji da kuma Boko Haram da ke mamaye wasu sassa na Arewa.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
