News
Ƴan bindiga sun kashe mutum 5 a Naija
Daga kabiru basiru fulatan
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Naija ta tabbatar da kashe jami’an ta uku da kuma ƴan vigilante 2 a wani harin kwanton-ɓauna da ƴan ta’adda su ka kai musu a Kwanan Dutse, Ƙaramar Hukumar Mariga a jihar.
Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Sunday Bala Kuryas ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ta wayar tarho.
Kuryas ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 4 na yamma lokacin da jami’an tsaro na haɗin gwiwa su ke sintiri a yankin.
Sai dai kuma a cewar sa, su ma jami’an sun hallaka ƴan ta’adda da dama a bata-kashin da a ka dau lokaci a na fafatawa.
Ya kuma ƙara da cewa, ko a ranar Lahadi, sai da rundunar tsaron ta haɗin gwiwa ta daƙile wani yunƙurin kai hari bayan an kwashe awanni biyu ana fafatawa da ƴan ta’addan a ƙauyen Bari, kan titin Tegina-Kontagora.
Ya kuma kara da cewa tuni rundunar ƴan sanda, ɓangaren sintiri na musamman da sojoji sun fara bibiyar ƴan ta’addan domin tabbatar da kame su.