Sports
Najeriya ta fi ko wacce kasa ƙoƙari a gasar Afcon – CAF
Daga muhammad muhammad zahraddin
Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta ce Najeriya ce kasar da ta fi ko wacce kasa kokari a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika da ake gudanarwa a Kamaru.
Wannan ya biyo bayan maki 9 da kasar ta hada a duka wasanninta da ta ci na rukuni, inda CAF a wani sakon Twitter da ta wallafa ta ce rabon da a nuna irin wannan bajinta tun 2010, lokacin da kasar Masar ta yi.
Yanzu dai Najeriya za ta hadu da kasar Tinusia a wasan gaba da za a fara bugawa a ranar Lahadi. A wani sakon na daban CAF ta wallafa cewa kocin Najeriya Augustine Eguavoen shi ne kocin da ya fi ko wanne kwarewa ya zuwa yanzua gasar.