News
Fiye da ƙungiyoyin matasa 40 a Kano sun nuna goyon bayansu ga takarar Yahaya Bello
Daga kabiru basiru fulatan
Fiyeda ƙungiyoyin matasa guda 40 ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya su ka yi kira ga tare da nuna goyon bayansu ga Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello akan ya fito takarar shugabancin ƙasar a babban zaɓen shekarar 2023 da ke tafe.
Ƙungiyoyin sun bayyana haka ne a lokacin da su ka gudanar da taron manema labarai a birnin Kano da ya gudana a jiya Talata, karkashin jagorancin Salisu Yahaya Manaja.
Salisu Manaja ya ce la’akari da irin ayyukan raya ƙasa da cigaban al’umma da Gwamna Yahaya Bello ya ke gudanarwa a jihar Kogi, shi ne dalilin da ya sa su ka yi kiran tare bayyana goyon bayansu.
“Gogewar sa da fice wajen ayyukan alkhairi ga jama’ar da su ka zaɓe shi da kuma ƙoƙarin sa ka mata a cikin gwamnatinsa na daga cikin dalilan da ya sanya mu goyon bayan sa”.
“Ya kasance matashi wanda ya ke da burin ganin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ya addabi Najeriya. Kuma shi gwamna ne da ya himmatu wajen taimakon ƴan kasuwa da kuma shigo da masu buƙata ta musamman cikin gwamnatinsa”.
Haka kuma Salisu Manaja ya ce kungiyoyin matasa guda 42 ne su ka nuna mubaya’ar ta su, da su ka haɗa da na cigaban matasa da na mata da na ƴan kasuwa da kuma ƙungiyoyin ɗalibai.
A ƙarshe ya yi kira ga sauran yan Najeriya da su taho a haɗu waje guda domin marawa Gwamna Yahaya Bello baya wajen kaiwa ga nasarar zama shugaban Najeriya a shekarar 2023.