News
Fyaɗe: Tagwaye sun yi wa ƴar shekara 10 taron dangi a Anambra
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
A na zargin wasu ƴan tagwaye, ƴan shekara 16 da haihuwa, Chukwuemeka da Chukwuebuka Okpe, da yiwa wata ƴar shekara 10 fyaɗe na taron dangi a Abagana, Ƙaramar Hukumar Njikoka ta Jihar Anambra.
Babbar Daraktar Gidauniyar Davina Care Foundation, Rachel Yohanna, ita ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Lahadi, a Awka, cewa mahaifiyar yarinyar, Benedict Sunday, wacce ma’aikaciyar jinya ce, ta kawo karar.
NAN ta samu labarin cewa waɗanda ake zargin ƴaƴan mai kula da gidan da yarinyar ta ke zaune da iyayenta ne inda a ka ce ƴan tagwayen sun ci gaba da cin zarafin ta sabo da taki yarda da su yi mata fyaɗe a karo na biyu.
Yohanna ta ce an kai rahoton laifin a ofishin ‘yan sanda na Abagana a ranar 16 ga watan Janairu, kuma an kama wadanda ake zargin da mahaifiyarsu, Chinwe Okpe.
Ta ce an kai yarinyar zuwa cibiyar binciken laifukan fyaɗe ta Ntasi da ke babban asibitin Enugu-Ukwu, inda aka tabbatar da cewa an ci zarafin ta kamar yadda wasu gurare a gabanta da bayanta su ka nuna.
Ta kuma ce an kai yarinyar, tare da rakiyar dan sanda da wata innar ta zuwa gwaji na biyu a asibitin ‘yan sanda, yayin da mahaifiyar wadanda ake zargin ta ce sakamakon asibitin Ntasi na jabu ne.
A cewar Yohanna, da sakamakon gwaji na biyun ya fito, sai ya nuna cewa lallai an yi wa yarinyar fyaɗe.
Yohanna ta ce a lokacin da ‘yan sanda ke yi mata tambayoyi, wadda abin ya shafa ta ce ‘yan tagwayen ne suka kai mata hari a bandaki yayin da mahaifiyarta ba ta nan, suka kwantar da ita a ƙasa su ka kuma yi mata fyaɗe.
“Yaran tagwayen har yanzu suna musanta cewa sun yi wa yarinyar fyaɗe,” in ji ta.
Yohanna ta ce yanzu haka yarinyar na ƙarƙashin kulawa yayin da aka mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na Akwa, domin ci gaba da bincike.
Ta ce za a gurfanar da tagwayen a gaban kotun shari’ar iyalai bayan bincike, yayin da gidauniyar za ta tattara tallafi da bin diddigin lamarin don tabbatar da cewa yarinyar ta samu taimakon jinya da kuma adalci,” inji ta.