News
Mutane 2 sun rasu a haɗarin kwale-kwale a Kano
Daga
muhammad muhammad zahraddin
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a cikin wani kogi, bayan da kwale-kwalen su ya nutse a Zangon Durgu zuwa kauyen Kanya da ke karamar hukumar Rimin Gado.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar, SFS Saminu Yusif, ya ce, an ceto biyu da ransu, yayin da wasu biyu kuma suka rasu nan take.
Ya ce, jami’an kashe gobara sun dauki matakin gaggawa ne, bayan da suka samu kira daga wani Barista Munir Dahiru, wanda ya kai musu rahoton faruwar lamarin da karfe 12:30 na ranar Litinin.
Ya kuma ce, mutane hudu ne lamarin ya rutsa da su, wanda suka ceto biyu sai dai kuma Sani Shitu mai shekaru 25 da Jabir Sabiu mai shekaru 30 sun rasa ransu a cikin ruwan.
Wadanda aka ceto sun hada da Sha’aban Bala mai shekaru 35 da Rabiu Bashari mai shekaru 30 a duniya, wanda suka mika su ga mataimakin shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Shafi’u Abdullahi Gulu domin tattaunawa da alakar su domin daukar mataki na gaba.
Yusif ya kuma shawarci daukacin mutanen da ke amfani da kwale-kwale da su yi taka tsan-tsan ta hanyar yin amfani da jirgin ruwan a yankunan su.