News
Mun ga ƴaƴan mu amma an ce ba namu ba ne, iyayen yaran Kano da a ka sace zuwa Anambra sun koka
Daga yasir sani abdullahi
Wasu da ga cikin iyayen yara 18 da a ke zargin an sace su a Jihar Kano kuma a ka kai su Jihar Anambra sun koka kan cewa sun ga ƴaƴan na su amma an hana su taho da su sabo da wai ba na su ba ne.
Iyayen sun ce hukumomin sun faɗa musu cewa ba za a basu yaran ba sabo da sakamakon gwajin ƙwayar halittar da a ka yi, wanda turanci a ke kira da DNA, ya nuna cewa ba ƴaƴan su ba ne.
Da su ke zantawa da Freedom Radio a Kano a jiya Laraba, cikin kuka da bacin rai, iyayen sun ce dama salon yin gwajin da a ka ce za a yi musu ya sanya su ke zargin cewa babu gaskiya a ciki.
A cewar su, lokacin da a ka je yin gwajin a can Anambra, an ce musu sakamakon gwajin zai ɗauki watanni shida kafin ya fito, amma sai bayan shekara ɗaya sannan a ka ce musu sakamakon ya fito kuma ya nuna cewa ba ƴaƴan su ba ne.
Shugaban ƙungiyar iyayen masu fafautukar nemo ƴaƴan su, Ismail Ibrahim Muhammad, ya baiyana cewa da a ka je ɗaukar yawun bakin iyayen su goma 16 a Anambra, an ce ka da su ci komai kafin a ɗauka.
A cewar sa, da su ka je wajen gwajin, bayan an ce kada su ci komai, amma sai su ka iske su yaran da suma za a ɗauki nasu yawun suna cin biskit.
Hakan, a cewarsa, wata maƙarƙashiya ce ta a hana su ƴaƴan su bayan da iyayen sun gan su kuma sun shaida su.
“Ta yaya za ai uwa ko uba ta ƙasa gane danta a ko ina ya ke kuka ko shekara nawa a ka ɗauka. Kawai dai mu ba mu yarda da wannan wuru-wurun da a ke nema a yi mana ba,”
Ya ƙara da cewa yara 18 a ka ce an gano a Anambra ɗin kuma iyaye 16 ne su ka je su ka gan su sannan sun tabbatar da cewa ƴaƴan su ne.
Ya kuma ce akwai yara sama da 100 da ba a gan su ba kuma an tabbatar su na can Anambra ɗin.
Iyayen dai sun yi kira ga gwamnatin Kano da ta shiga maganar domin su samu a dawo musu da ƴaƴan su.
A 2019 ne dai a ka gano wasu yara su 9 da a ka sace a Kano a ka kai su Anambra, inda a ka sayar da su da kuma canja musu addini, lamarin da ya daɗe ya na haifar da cece-kuce a faɗin ƙasar nan.
Tun a lokacin dai iyaye su ke ta fitowa su na ƙorafin cewa an sace musu ƴaƴan su, inda su ke zargin ko suma an kai su Anambra ɗin, shine su ke kira ga gwamnatin Kano da ta shiga lamarin ta kuma kawo musu ɗauki.