Daga Muhammad Muhammad zahrad

Wasu dakarun Amurka na musamman sun kai hari a arewa maso yammacin Syria inda suka kashe shugaban kungiyar Islamic State (IS) da ke ikirarin jihar,a cewar shugaba Joe Biden.

“Muna godiya bisa basira da kwazon sojojimu, mun kawar da Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi,” a cewar sanarwar da ya fitar.

Advertisement

Wani babban jami’in kasar Amurka ya shaida wa kafafen watsa labarann kasar cewa Qurayshi ya tayar da bam din da ke jikinsa inda ya kashe kansa da iyalansa.

Wasu ‘yan Syria da suka soma zuwa wurin da lamarin ya faru sun ce sun ga gawarwaki 13 bayan harin.

Jiragen helikwafta da dama na Amurka sun sauka a wajen garin Atmeh da ke hannun ‘yan tawaye, wanda yake lardin Idlib na arewacin kasar da ke kusa da kan iyakar kasar da Turkiyyas, da kusan tsakar daren Alhamis a agogon kasar.

Advertisement

Majiyoyi sun ce dakarun sun fuskanci turjiya sosai kuma an bude musu wuta da manyan bindigogi da aka girke a kan motoci.

An ji karar musayar wuta da kuma harba makamai tsawon awa biyu kafin jiragen masu saukar ungulu su bar wurin.

Jaridar New York Times ta rawaito cewa an bar wani jirgi mai saukar ungulu da ya lalace, amma daga bisani sojojin Amurka suka lalata shi . An sanya hotunan jirgin a shafukan intanet.

Advertisement

Shugaba Biden ya ce dukkan Amurkawan da suke da hannu wajen kai harin sun koma gida ba tare da ko kwarzane ba, wwanda ya ce an kai shi ne domin “kare Amurkawa da kawayenmu, sannan a raba duniya da miyagun mutane”.