News
Ƴan bindiga sun hana ɗauko gawarwakin waɗanda suka kashe a Maru don yi musu jana’iza
Daga yasir sani abdullahi
Kwana huɗu bayan kai wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 12 a ƙaramar hukumar Maru cikin jihar Zamfara, har yanzu ‘yan bindiga sun hana a je a ɗauko gawarwakin don yi musu jana’iza.
Harin na ranar Juma’a a Daraga, ya yi sanadin tarwatsewar mazauna garin zuwa gudun hijira.
‘Yan sanda a Zamfara sun ce suna ƙoƙarin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Latsa hoton da ke sama domin sauraren rahoton da wakilin BBC Abdussala Ibrahim Ahmed ya hada kan batun..