News
Mutumin kirki nake so ya gaji kujerata a 2023. Gwamna Badaru
Daga yasir sani abdullahi
Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar yace yana fata ganin an samu mutum mai kamala a matsayin wanda zai lashe kujerar sa a shekarar 2023.
Badaru wanda yanzu haka yake zangon sa na karshe a mulkin jihar, bayan da aka zabe shi a shekarar 2015, kana kuma ya kara lashe mulki a 2019.
Badaru ya bayyana haka ne bayan da wata kungiya mai suna £Hadeja Ina Mafita” ta karramashi a safiyar ranar litinin din nan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
“Addu’a ta shi ne samun mutum mai kima, wanda yake da tsoron Allah, kuma zai dora daga inda muka tsaya, tare da sauraron halin da jama’a suke ciki”, Inji Badaru.