Connect with us

News

An kashe matar aure a cikin gidanta a Kano

Published

on

FB IMG 16448255036485009
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Mutanen unguwar Danbare da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano sun shiga tashin hankali da alhini bayan da a ka iske an kashe wata matar aure, mai suna Rukayya Mustapha a cikin gidan aurenta.

Advertisement

Jaridar indaranka ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a yammacin Asabar, inda makasan na Rukayya su ka kuma ji wa ƴaƴanta biyu ƙanana rauni.

Wannan jaridar ta kuma jiyo cewa an yi amfani da taɓarya ne a ka buga wa marigayiyar a kanta, inda ta ce ga garin ku nan.

Ba a san ya a ka yi makasan su ka shiga gidan ba duk da cewa, an ce a kwai wasu masu aikin gini a maƙotan gidan da abin ya faru.

Advertisement

An ce ba wanda ya san mai ya faru har sai da mijin ta ya dawo da ga kasuwa sannan ya tarar da ita a kwance ta mutu.

Da wakilin mu ya kira Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai samu ya amsa wayar ba.

Sai dai kuma BBC Hausa ta rawaito cewa SP Kiyawa ya ce rundunar ta kama mutane biyar da a ke zargi da hannunsu a kisan.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *