News
Yanzu-Yanzu: ASUU ta ayyana Pantami a matsayin Farfesan bogi
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kungiyar bayan taronta na Majalisar Zartaswa ta kasa ta ayyana karin girman a matsayi na Farfesa an yi ne “ba bisa ka’ida ba”.
An bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya yi jawabi a ranar Litinin kamar yarda Daily True Hausa ta ruwaito.
Ya ce, “Ba za ka iya zama minista kuma ka zama malami a jami’a ba.
“Dole ne Pantami ya ajiye aiki a matsayin minista kuma a sake gwada shi saboda Bai cancanta ba, Bai kamata a dauki Pantami a matsayin farfesa ba.”
A watan Satumbar 2021, Majalisar Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Owerri ta daukaka Pantami, tare da malamai bakwai zuwa matsayin farfesa a taron majalisar karo na 186.
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News3 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
