Connect with us

News

Kotu ta yanke wa korarrun ƴan sanda 2 hukuncin kisa sakamakon yin fashi da makami

Published

on

FB IMG 1645129942855
Spread the love

Daga aminu usman jibrin

 

 

Advertisement

A yau Alhamis ne Mai Shari’a Peter Kekemeke na Babbar Kotu a Abuja ya yanke wa wasu korarrun ƴan sanda guda biyu hukuncin kisa sakamakon aikata fashi da makami.

Waɗanda a ka yanke wa hukuncin su ne James Ejeh da Simeon Abraham.

An gurfanar da su je a gaban Alƙali a ranar 20 ga watan Oktoba, 2017 a bisa kaifuka biyu da su ka haɗa da haɗin baki da fashi da makami.

Advertisement

Da ya ke yanke hukunci, Kekemeke ya ce mai ƙara ya gamsar da kotu ba tare da wani haufi ba bayan ya kira shaidu huɗu.

Alƙalin ya ƙara da cewa shaidu da a ka gabatarwa kotun sun tabbatar da cewa waɗanda a ke ƙarar sun aikata fashi tare da makami a hannayensu.

Ya kuma ƙara da cewa sun amsa laifin na su kuma babu wata shaida sama da amsawar da su ka yi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *