News
Mahadi Aliyu: ‘Yan majalisa na son tsige ni daga mataimakin gwamnan Zamfara ne saboda na ƙi komawa APC

Daga kabiru basiru fulatan
Mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, wanda ake shirin tsigewa ya ce ana yi masa bita-da-ƙulli ne saboda ya ki bin gwamnan jihar Bello Matawalle zuwa jam’iyyar APC.
Ranar Litinin din nan ne kwamitin da babbar mai shari’a ta jihar ta kafa zai zauna don jin bahasin mataimakin gwamnan, game da wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.
Sai dai yayin wannan hira da BBC, ya fito fili ya ce ba zai amsa gayyatar da aka yi masa ba, domin an saɓa doka wajen bin ka’idar tsige shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi.