News
Za a yi zaɓen shugaban Najeriya ranar 25 ga Fabarairun 2023

Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.
A cewarsa, an zaɓi ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri’a.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran ranakun da za a gudanar da zaɓukan “a lokacin da ya dace”.
Ƙarin bayani na nan tafe…