News
Ganduje ya bada kyautar N3m ga ɗalibin da ya ci maki 303 a JAMB
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa wani dalibi, Suyuɗi Sani, ɗan asalin jihar, da ga Ƙaramar Hukumar Nassarawa kyautar Naira Miliyan 3 sakamakon ƙwazon da ya yi na samun maku 303 a jarabawar JAMB.
Ɗalibin ya zama shine na biyu a ƙasa baki ɗaya.
A sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan Kano, Abba Anwar ya fitar a jiya Litinin, gwamnan ya bada kyautar ne a yayin ganawar majalisar zartaswa ta mako-mako a gidan gwamnati.
Ganduje ya yaba wa ɗalibin a bisa ƙwazon da ya yi, inda ya ƙara da cewa aikin gwamnati ne ta riƙa tallafa wa irin haziƙan daliban domin ƙara musu ƙarfin gwiwa.
Gwamnan ya kuma yi alƙawarin baiwa Sani tallafi karatu kyauta har zuwa matsayin digirin-digirgir, inda ya ƙara da cewa hakan zai sanya wa ƴan baya ƙaimi su ma su dage su riƙa ƙoƙari a jarabawar.