News
Komawar matasa harkar noma shine zai kawo karshen rashin aiki a Nigerian-Aminu ya,u Muhammad.

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Komawar matasa harkar noma zai samar da aiyukan yi a kasa baki daya,kasan cewa manyan kasashen duniya suma suna dogara ne da harkar noma .
Aminu ya,u Muhammad yabaiyana hakan ne yayin tautauna warsa da wakilin mu Muhammad Muhammad zahraddin yace matasan yanzu sun dau noma a matsayin harkar wahala duk da yana yin da ake ciki a yanzu na rashin aikin yi.
Ya kara da cewa yakamata matasa suyi amfani da damar su wajan samar wakan su hakar dogaro da kai da kuma ciyar da kasa baki daya ta hanyar noma
Dan haka ina kira ga matasa dasu hararci taron da suka shirya da kungiyar ALL FARMERS ASSOCIATION OF NIGERIA (AFAN) wanda za’a gudanarwa kamar haka:-24/03/2022 DA MISALIN KARFE 10:00am Na Safe A MUMBAYYA HOUSE don nunawa masata sabuwar hanyar koyan harkokin noma ta hanyar zamani domin suyi dogaro da kansu da cigaban kasa baki daya.
Daga karshe yayi kira ga matasa dasu daina raina sana,ar noma dan tana da tarihi a kasar mu Najeriya.
