Connect with us

News

Yayin da Buhari ke ci gaba da zama a Landan, Najeriya ta shiga cikin duhun wutar lantarki

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

Advertisement

 

Bayan da aka kwashe makonni ana samun sauyin wutar lantarki a Najeriya, a ranar 15 ga watan Maris, An tabbatar da rashin wutar lantarki a fadin kasar.

Advertisement

Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki (GenCos), sun sanar a shafinsu na Twitter da kuma gidan yanar gizon su cewa na’urar wutar lantarki ta kasa ta gamu da tasgaro.

Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ci gaba da zama a Landan a ziyarar da ya shafi lafiya kuma uwargidan sa Aisha a Dubai, Najeriya ta shiga cikin duhu.

Advertisement

Kungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki, APGC, a ranar Lahadin da ta gabata, ta dora alhakin rashin gudanar da aikin samar da wutar lantarkin ga Kamfanin TCN, a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke haddasa karancin wutar lantarki a kasar.

A halin da ake ciki a harkar hada-hadar kasuwanci, kamfanonin samar da wutar lantarki (Gencos) a karkashin kungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki (APGC) a jiya sun yi ikirari da cewa matsalar wutar lantarki ta kara ta’azzara a kasar nan domin ana bin su sama da Naira tiriliyan 1.6 tun daga shekarar 2013.

Advertisement

Don kara wa jama’a kuncin rayuwa, wannan bala’i ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar kasar ke fama da matsanancin karancin man fetur da farashinsa ya yi tsada.

Idan dai ba a manta ba, bangaren samar da wutar lantarkin da ba a iya dogaro da shi ba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulki tare da alkawarin gyara bangaren wutar lantarki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending