Connect with us

News

YANZU-YANZU: Ƴan bindiga sun saka bam a gidan shugaban Ohaneze a Imo

Published

on

Daga maryam bashir musa

 

 

 

A safiyar yau Asabar ne dai wai ƴan bindiga su ka ƙone gidan Babban Shugaban kungiyar inyamirai ta Ohaneze Ndigbo, Farfesa George Obiozor a Awo-Omanma, Ƙaramar Hukumar Oru ta Kudu a Jihar Imo.

An kiyo cewa maharan da su ka zo gidan Shugaban a ababen hawa, sun jefa bamabamai cikin gidan.

Advertisement

Sai dai kuma rahotanni sun baiyana cewa Obiozor ba ya gidan lokacin da s ka kai masa harin.

Wata majiya da ga gidan ta baiyana cewa na’urar ɗaukar hoto ce ta naɗi harin da a ka yi lokacin da shi Obiozor ɗin ba ya gidan.

Har yanzu dai Shugaban bai yi magana ba amma wani da ga cikin makusantan sa, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya kira shi ya yi masa jaje.

Ya kuma yi kira ga ƴan sanda da su tashi tsaye su kamo waɗanda su ka kai harin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending