News
Shugabannin Izala sun kai wa mataimakin shugaban ƙasar Ghana ziyara
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Shugabannin ƙungiyar Izala a Najeriya sun kai ziyara ƙasar Ghana inda suka gana da mataimakin shugaban ƙasa Mahamudu Bawumia
Babban sakataren kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS),Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya wallafa hotunan ziyarar a Twitter.
Hotunan sun nuna shi tare shugaban ƙungiyar Shiekh Abdullahi Bala Lau a gidan mataimakin shugaban Ghana.
Shiekh Gombe ya ce mataimakin shugaban Ghana ne ya gayyace su domin tattauna batutuwan da suka shafi harakokin addinin Islama.
Ya kuma ce sun halarci wani bikin ƙaddamar da sabuwar makarantar koyar da aikin jinya ta Musulunci a Ghana.
Hotunan da malamin ya wallafa sun nuna ginin cibiyar bene hawa uku inda hawa na biyu ke ɗauke da sunan “Sheik Haruna Kabiru Gombe”, hawa na uku kuma yana ɗauke da sunan “Sheik Abdullahi Bala Lau.”
Hawa na farko na ɗauke ne da sunan marigayi “Sheik Abubakar Gummi”
