Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya za ta raba ɗalibai miliyan 10 da tsutsar ciki

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Ma’aikatar da ke kula da jin adadin al’umma ta Najeriya ta ce za ta fara aikin raba ɗalibai da tsutsar ciki a makarantun kasar, inda ta ce fiye da ɗalibai miliyan 10 ne za su amfana da wannan shirin.

Ma’aikatar ta kuma ce za ta gudanar da wannan aikin ne hannu da hannu da wanda ta ke yi na ciyar da ɗalibai a makarantun gwamnati na ƙasar.

Babban jami’i a sashen da ke kulawa da ayyukan jin dadin al’umma na ma’aikatar, Dakta Umar Bindir ne ya sanar da haka yayin wani taro na kwana biyar da ke gudana a Abuja ta hannun babbar jami’a mai kula da sashen tsare-tsare da bincike ta ma’aikatar, Safiya Sani wadda ta wakilce shi a wajen taron.

Dakta Umar ya ce za a raba ɗaliban ne da tsutsotsin ciki domin inganta lafiyarsu.

Ya kuma ce aikin zai shafi ɗalibai ne daga aji na ɗaya zuwa aji na shida na firamare, musamman waɗanda ke makarantun gwamnati.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending