Connect with us

News

Gwamnatin Taraiya za ta tallafawa yaran da ba sa zuwa makaranta 72,000 a Naija

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga hafsat abdullahi Suleiman

 

 

 

Gwamnatin Jihar Naija ta ce ta shiga tsarin Gwamnatin Taraiya mai taken At-Risk Children Project, ARC-P da za a tallafawa sama da yara 72,000 da ba sa zuwa makaranta.

Wacce ta shirya shirin kuma mai dakin gwamnan jihar Naija, Dakta Amina Bello ce ta baiyana hakan a Mina, lokacin da ta karbi baƙuncin tawogar ARC-P, bisa jagorancin Maryam Uwais, mai baiwa shugaban kasa shawara a kan shirye-shiryen tallafawa al’umma.

Advertisement

Dakta Bello ta ce gwamnatin jihar za ta yi amfani da shirin domin tallafawa yaran da ba sa zuwa makaranta d akuma magance zaman-banza tsakanin matasa a faɗin jihar da kuma samar musu da sana’o’in da za su riƙe su tsawon rayuwarsu.

Ta danganta matsalolin rashin tsaro da ke gallabar Arewacin Nijeriya da talauci, inda ta ce amfanin shirin ARC-P kenan wajen magance waɗannan laifukan.

Ta ce gwamnatin jihar ta dage wajen tallafawa yaran da basa zuwa makaranta domin daga darajar rayuwarsu su zama masu amfani a cikin al’umma.

A nata jawabin, Uwais ta ce an ƙirƙiro da shirin ne domin ya baiwa gwamnati damar tallafawa yaran da basa zuwa makaranta ta hanyoyi daban-daban.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending