News
Mahara Sun Daka Wawa Kan Dukiyoyin Jama’a A Kudancin Kaduna
Wasu mahara sun kai farmaki a kauyukan Kabode da Ankuwa da ke da nisan kilomita 10 daga garin Kachia, a Kudancin Jihar Kaduna tare da sace musu kayayyaki.
Majiyar Aminiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce maharan sun shiga yankunan ne a kan babura da yawa da misalin karfe 9:20 na dare, sannan suka fara bude wuta kan mai uwa da wabi.
’Yan bindiga sun sace jami’in Kwastam da wasu mutum 9 a Zariya
Gobara ta kone shaguna sama da 300 a kasuwar Abuja
Majiyar ta ce, “Wannan shine karo na biyar tun shekarar da ta gabata da maharan ke kawo mana hari suna karbar kudin fansa.
“A baya ma sai da suka saka mana biya harajin biyan har Naira miliyan biyar kan ba za su sake kawo mana hari ba, sai ga shi sun dawo bayan an ba su abinda suka bukata,” inji majiyar.
Zuwa yanzu dai, mutanen yankunan na ta yin kaura suna barin gidajensu don tsira da rayukansu.
Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai amsa wayar sa ba kuma bai amsa rubutaccen sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya tura masa ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
