Connect with us

News

Nijar za ta ɗauki ƙarin sojoji 5,000 maimakon 2,000

Published

on

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da shirin ɗaukar sabbin dakarun soja 5,000 a rundunar sojan ƙasar a yaunƙurin gwamnati na yaƙar ‘yan bindigar da ke addabar yankuna daban-daban na ƙasar.

Matakin na zuwa ne yayin da Boko Haram ke ƙara tsaurara hare-hare a garuruwan da ke kudancin ƙasar masu iyaka da Najeriya da kuma ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ƙawayen IS da al-Ƙa’ida a yammaci da ke da iyaka da Mali da Burkina Faso.

Advertisement

Akasari dai gwamnatin Nijar na ɗaukar mutum 2,000 ne duk shekara a aikin soja.

Hukumomi sun nemi matasa ‘yan shekara 18 zuwa 25 da su gabato da kansu don shiga aikin tsaron na soja da zummar kare ƙasarsu.

Advertisement

A cewar wata sanarwar gwamnati, za a fara ɗaukar sabbin dakarun daga watan Mayu mai zuwa.

Ficewar sojojin Faransa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Mali ta jawo giɓi na tsaro bayan shafe shekara kusan 10.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending