Connect with us

News

NDLEA ta kama hodar ibilis a zanin gado

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta kama ƙunshin hodar ibilis ko kuma koken a filin jirgin sama na Fatakwal da ke Jihar Rivers a kudancin Najeriya.

NDLEA ta wallafa wani bidiyo a yau Lahadi da ta ce yana nuna yadda masu safara suka ɓoye ƙunshi 73 na koken ɗin a cikin zanin gado.

Kazalika, hukumar ta ce ta ƙwace ƙwayar tramadol miliyan tara da rabi a Legas da ta kai darajar naira biyan biyar.

Advertisement

Hakan nan, hukumar ta ce ta kama mutum bakwai a Kano saboda zargin su da mu’amala da miyagun ƙwayoyin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending