Connect with us

News

IRDOGAN YA NUNA BACIN RANSA AKAN HARIN MASALLACIN KUDUS.

Published

on

Daga khadija Abdullahi Mahmud.

 

Shugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana matukar bacin ransa da tashin hankalin da ake samu a Masallachin Al Aqsa dake Birnin Kudus, lokacin da ya tattauna ta waya da shugaban Israila Isaac Herzog.

Kalaman Erdogan na zuwa ne bayan arangamar da aka samu tsakanin Yahudawa da Falasdinawa a ciki da wajen Masallachin, wanda ya kaiga raunata mutane sama da 170 akasarin su Falasdinawar dake zanga zanga saboda matakan da jami’an tsaron Israila ke dauka.

Wannan tashin hankalin na zuwa ne kusan shekara guda da irin sa da aka gani wanda aka kwashe kwanaki 11 ana fafatawa tsakanin Israila da Falasdinawa masu tsatsauran ra’ayi dake Gaza.

Masallachin Al Aqsa na da matukar muhimmanci ga mabiya addinin Yahudawa, yayin da kuma shine wurin ibada mafi kima ga Musulmi bayan Masallachin Makkah da na Madinah.

Advertisement

Tashin hankalin da aka samu a karshen mako ya sanya Israila amfani da karfi wajen kai harin sama Yankin Gaza da kuma tura sojojin ta domin farautar masu tsatsauran ra’ayi a Yankunan Falasdinawa.

Erdogan yace hotunan da suke gani na yadda ake kaiwa Falasdinawa hare hare a Masallachin abin Allah wadai ne, wanda ke iya samun martani daga kasashen Musulmin duniya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending