News
AN TSARE MINISTAN SADARWA NA NIJAR SABODA BATAN KUDADEN GWAMNATI
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun tsare ministan sadarwar kasar Mahamadou Zada inda ake tuhumarsa da almubazzaranci da kudaden talakawa lokacin da ya jagoranci wata hukumar gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace ma’aikatan shari’a ta yiwa Zada tambayoyi dangane da zargin da ake masa na bacewar kudin da ya kai kusan Dala miliyan 6 daga hukumar dake kula da ayyukan hakar ma’adinai wanda ya jagoranta tsakanin shekarar 2013 zuwa shekarar 2021.
Kafofin yada labaran Nijar sun ce a shekarar da ta gabata aka bankado bacewar kudaden, abinda ya sa kaddamar da bincike akan lamarin.
Kafofin yada labaran cikin gidan Nijar sun ce wannan badakala ta samo asali ne a shekarar da ta gabata, lokacin da kamfanin Taanadi, da yayi fice wajen bayar da lamuni, ya ce ya kasa gano CFA biliyan uku da kamfanin Sopamin ya ce an aika cikin asusunsa.
Shekaru goma da suka gabata, kamfanin Sopamin ya shiga cikin wata badakala da ta shafi cinikin Uranium na kasa da kasa da Kamfanin Areva ta Faransa ya shirya wanda a yanzu aka sauya masa suna zuwa Orano.
