News
Muna aiki tukuru don ceto Mutanen da aka sace a jirgin kasan Kaduna-Abuja – Buhari
Daga maryam bashir musa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa iyalai da ‘yan uwan mutanen da aka sace daga jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna cewa za a dawo da ‘yan uwansu gida ba tare da matsala ba.
Ya bayyana haka ne a yayin da wasu al’ummar Abuja suka kai masa gaisuwar Sallah ranar Litinin a fadarsa ta Aso Villa.
Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya fitar ta ambato shugaban kasar yana cewa ‘yan bindigar suna amfani da mutanen da suka kama ne a matsayin wata garkuwa.
“A yayin da muke murnar wannan lokacina farin-ciki a tsakanin abokai da iyalai, muna sane cewa iyalai da dama a kasarmu suna cikin yanayi na tsoro da zaman dar-dar sakamakon sace ‘yan uwansu da ‘yan ta’adda suka yi, cikinsu har wadanda aka sace bayan an sanya bam a jirgin kasan Abuja – Kaduna.
“Na bai wa jami’an tsaro umarni su yi gaggawar kubutar da su daga hannu masu satar mutane cikin koshin lafiya,” in ji Buhari.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
