Connect with us

News

2023: ‘Yan APC a yankin Yarbawa za su zauna, su hada kai su zabi mai gaje Buhari daga yankinsu

Published

on

 

Rahotanni da ke fitowa a yankin Kudu maso Yamma na nuni da cewa, jiga-jigan yankin za su yi amfani da ikonsu wajen hade kan ‘yan APC Manufar hada kai da taron da za su yi shi ne a samar daya kwakkwara daga yankin wanda APC za ta ba tikitin takara na 2023 Sai dai, kusan dukkan yankunan kasar nan na ci gaba da nuna sha’awar samar da dan takara tilo a zaben mai zuwa

Jihar Legas – Shugabanin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Yamma za su gana da masu neman takarar shugaban kasa na yankin a ranar Juma’a a jihar Legas, kamar yadda jaridar WesternPost ta ruwaito. An bayyana cewa taron zai gudana ne a gidan gwamnatin Legas.

TheCable ya bayyana cewa Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC ne zai jagoranci taron. 2023: ‘Yan APC a Kudu maso Yamma za su hada kai su zabi mai gaje Buhari daga yankinsu

An ce shugabannin yankin sun damu matuka da yawan masu neman tikitin jam’iyyar APC daga yankin Kudu a zaben 2023 mai zuwa.

Wadanda aka gayyata taron dai sun hada da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da gwamnonin jam’iyyar APC na shiyyar da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice da sauran shugabannin APC na shiyyar, inji Daily Trust.

Advertisement

manyan yankin Yarbawa Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas; Kayode Fayemi; Gwamnan Ekiti; da Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan Ogun, na daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu maso Yamma.

Makasudin taron dai shi ne a fitar da tsare-tsare don ganin cewa yankin Kudu maso Yamma bai rasa tikitin takarar ba saboda yawan masu fatan gaje Buhari da suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takara, kamar yadda aka bayyana.

Majiya ta bayyana cewa: “Akande, wanda ake mutuntawa a duk bangarorin siyasar a yankin, da sauran wadanda suka kira taron suna son ganin an rage jerin sunayen ‘yan takarar Kudu maso Yamma domin kada yankin ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na APC.” “

Shugabannin sun damu cewa idan yankin Kudu maso Yamma bai samu hadin kai ba, muna iya rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zuwa wani yanki. Abu ne da ya fi daukar hankali a ce ‘yan jam’iyyar APC guda hudu ‘yan inuwar siyasa daya ne. “Kudu-maso-Gabas na yin mai yiwuwar tsayar da dan takarar shugaban kasa.

Hatta Kudu-maso-Kudu da suka yi Shugaban kasa da a baya-bayan nan; Shugaba Jonathan, suna son a sake basu dama ganin ‘yan takara na fitowa daga yankin.”

A halin da ake ciki dai, jam’iyyar APC ba ta dau wani mataki a hukumance ba kan batun inda za ta mika tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2023 mai zuwa ba, amma na ci gaba da kai ruwa rana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending