News
Kotu ta ƙi ba da belin Nnamdi Kanu
Daga idriss Hussaini Nguru
Babbar kotun tarayya a Abuja, Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra IPOB da ake tsare da shi, Nnamdi Kanu ta neman a bayar da belinsa, har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci kan laifin cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ke tuhumarsa.
Mai Sharia Binta Nyako, ta yi watsi da buƙatar belin tana mai cewa kotu ba za ta bayar da belinsa ba saboda ya taɓa saɓa belin da aka ba shi a 2017. Ta ce kotu na son sanin dalilin da ya sa ya saɓa belin farko kafin har ya sake neman wani.
Kafin zaman kotun a ranar Laraba, Ƙungiyar IPOD da aka haramta a Najeriya ta tilasta dokar zama gida a faɗin yankin kudu maso gabas domin nuna goyon baya ga shugabanta.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
