Shugaban kasar Senegal, Macky Sall, ya kori ministan lafiya na kasar, Abdolaye Diouf, bayan da wata gobara ta kashe jarirai goma sha daya a wani asibitin yankin ranar Laraba.
Marie Kemesse Ndiaye za ta maye gurbin Abdolaye Diouf.
Ana alakanta gobarar da ta mamaye sashen haihuwa da ke asibitin da haduwar wayoyin lantarki.
Shugaban kasar ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.
Kazalika ya ayyana makokin kwana uku.
