News
Da Ɗan bindiga da ‘Deliget’, Ɗanjuma ne da Ɗanjummai – Shehu Sani
Daga yasir sani Abdullah
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce babu maraban ƴan bindiga da ‘Deliget’ a siyasan Najeriya.
An kori Ministan Lafiya saboda mutuwar jarirai a wani asibiti
Shehu Sani ya bayyana cewa yadda mahara ke karɓar kuɗi a hannun waɗanda suka yi garkuwa da haka suma ‘Deliget’ ke karvar irin wannan kuɗade a hannun mutane da sunan wai za su zabe su.
” Na shiga siyasa ne domin a gyara tsarin a tsaftace shi ta yadda za a rika zaɓen nagartattun mutane waɗanda suka cancanta ta hanyar yin zaɓen mai aminci da nagarta tun daga zaɓen ƴan takara zuwa zaɓen shugabanni.
” Ni fa a ganina ban faɗi zaben fidda gwani ba, ban yi nasara ne a kasuwanci siye da siyarwar ɗan takara ba ta hanyar wanda yafi zabga kuɗi ya kwashi dami.
” Bai kamata ace wai ta irin wannan hanya ce za a riƙa zaɓen waɗanda za su shugabanci jama’a a kasar nan ba, saboda maimakon a zaɓi nagari mai dammai a aljihu ne za a baiwa mulki ko mai lalacewar sa kuwa. Hakan bai dace ba.
” Gaba ɗaya turbar siyasar kasar nan a gurɓace ta ke, hanyar zaɓen ɗan takara ta hanyar zabe na ‘Deliget’ hanya ce kawai da ya bada damar dora ruɓaɓɓu, gurbatattun ƴan siyasa karagar mulki cikin sauki ta hanyar watandar miliyoyin kuɗi.
” Idan ba mun dawo daga rakiyar siyasar mai-kudi-ɗauka bane komai munin sa ba za mu taba ɓanɓaro ƙasar nan daga bangon ginin cuwacuwa, almundahana, karfakarfa ba, sannan kuma matasa sai dai su ji a salansa amma ba wai su iya shiga a fafata da su ba
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News23 hours ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
