Connect with us

Politics

Dole na ceto Najeriya daga rashin iya mulkin APC na shekaru bakwai – Atiku Abubakar

Published

on

Atiku

Daga yasir sani Abdullahi

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ɗan takarar shugaban kasa a ƙarkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ya ɗaura ɗamarar fara yaƙin neman zaɓe domin tabbatar da karɓe ragamar Najeriya a 2023, da kuma ceto ƙasar daga rashin iya mulki irin na APC cikin shekaru bakwai.

 

Advertisement

Ɗan takarar ya bayyana haka ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta mika wa Atiku Abubakar shaidar zama ɗan takarar ta a zaɓe mai zuwa.

 

Advertisement

Ya kuma jadada amfanin haɗin kai da aiki tuƙuru da kowanne ɗan kasa wajen cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

 

Advertisement

Yana mai cewa akwai ayyuka da dama kuma lokacinsu na kurewa don haka dole a nuna jajircewa

 

Advertisement

An zaɓi Atiku Abubakar ne a zaben fitar da gwamni na PDP da aka gudanar a ranar Asabar din ƙarshen mako.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending