Connect with us

Politics

Rikicin APC: Sanata Abdullahi Adamu ya bada haƙuri

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyar APC na ƙasa, ya bada haƙuri a kan rikicin da ya kunno kai a kwanan nan.

Ku riƙa tuƙin keke domin samun lafiyar jiki, FRSC ta shawarci ƴan Nijeriya

Advertisement

 

Jaridar Indaranka ta rawaito cewa kwanaki uku da su ka gabata ne dai wasu masu riƙe da muƙamai a APC, Mataimakin Shugaban Jam’iya, Arewa-maso-Yamma, Mallam Salihu Lukman da takwaransa na Kudu-maso-Yamma, Isaac Kekemeke su ka zargi Adamu da ajiye su a gefe a al’amuran jam’iyyar ba tare da yi da su ba.

Advertisement

 

Sun zargi Adamu da yin abubuwa da dama waɗanda ba su dace ba a shugabancin jam’iyar, inda su ka nuna ɓacin ransu kan yadda ya ke ɗaukar matakai shi kaɗai ba tare da aiki tare da sauran nataimakansa ba

Advertisement

 

Sai dai kuma rahotanni sun baiyana cewa, a wata ganawa mai tsawo da ya yi da shugabanni da masu ruwa da tsaki na APC a Abuja a jiya Laraba, Sanata Adamu ya fito fili ya amsa laifinsa.

Advertisement

 

Hakazalika Sanata Adamu ya baiwa duk wanda a ka ɓata wa haƙuri, inda ya yi alƙawarin gyara kurakurensa da kuma tafiya da kowa a wajen tafiyar da al’amuran jam’iyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending