Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai Uefa ta nemi afuwar ƙungiyoyin Real Madrid da Liverpool bayan magoya bayansu sun shiga halin tasku lokacin kallon wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Champions League da Madrid ta lashe.
Uefa ta ce lamarin ba zai sake faruwa ba nan gaba.
Magoya bayan Liverpool sun bayyana cewa ‘yan sanda sun ƙuntata musu, da haddasa yamutsi a wasan da aka buga ranar Asabar da ta gabata.
“Bai kamata a saka duk wani dan kallo cikin irin wannan hali ba kuma hakan ba za ta sake faruwa ba,” a cewar wata sanarwa ranar Juma’a.
Neman afuwar ya biyo bayan suka da caccaka daga magoya baya a faɗin duniya game da yadda aka hana wasu da dama shiga filin wasa na Stade de France don kallon wasan duk da cewa suna da tikiti.
‘Yan sandan Faransa sun ce wasu sun yi yunƙurin shiga ba tare da tikiti ba, abin da ya jawo aka jinkirta take wasan da fiye da minti 30.
