Connect with us

Entertainment

Ya Maka Hadiza Gaban A Gaban Kotu Saboda Ta Ki Auren Shi

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wani maigidanci mai kimanin shekara 48 ya maka jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Hadiza Gabon, a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna saboda ta ki amincewa ta aure shi.

 

Advertisement

Maigidancin, mai suna Bala Musa, wanda ma’aikacin gwamnati ne ya shaida wa kotun cewa sun jima suna soyayya da jarumar, bisa alkawarin za ta aure shi, amma ta ci gaba da yaudarar shi.

Koriya ta Arewa zata sake gwada makamin nukliya

Advertisement

‘Lalacewar tashoshin samar da wutar lantarki 20 ne ya janyo rashin wuta a Najeriya’

 

Advertisement

 

Bala ya ce, “Ya zuwa yanzu, na kashe mata N396,000. Duk lokacin da ta tambaye ni kudi na kan kashe mata ba bata lokaci cikin fatan za ta aure ni.

Advertisement

 

“Amma ko da na gayyace ta zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara inda nake da zama, sai ki zuwa,” inji Bala Musa.

Advertisement

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an fara sauraron karar ce tun a ranar 23 ga watan Mayun 2022, amma Hadizan ba ta halarci zaman kotun ba.

Advertisement

 

Lauyan jarumar, Mubarak Kabir, ya shaida wa kotun cewa wacce yake karewa ba ta halarci zaman ba ne tun a lokacin saboda rashin sanin sahihancin takardar sammacin da aka kai mata.

Advertisement

 

Ya ce, “A matsayin wacce nake karewa na shahararriya, mutane da yawa kan je wajenta da manufofi iri-iri. Tana taka-tsan-tsan ne da lafiyarta.”

Advertisement

 

Daga nan sai ya roki kotun da ta ba shi karin lokaci don ya gabatar da ita a gaban kotun.

Advertisement

 

A nan ne alkalin kotun, Mai Shari’a Rilwanu Kyaudai, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending