News
An sace ƴan kasuwa ‘kusan 40’ a hanyar Sokoto zuwa Zamfara
Daga yasir sani Abdullah
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace kusan mutum 40 a hanyar zuwa Jihar Zamfara daga Sokoto.
Jama’ar da aka sace akasarinsu masu sana’ar sayar da wayoyin sadarwa ne a kasuwar Bebeji Plaza da ke Jihar Zamfara. Rahotanni sun ce sama da mutum 60 ne ƴan bindigar suka tare a hanyar, amma sama da 20 sun samu sun kuɓuta.
Shugaban kasuwar ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce an yi garkuwa da ƴan kasuwar ne a hanyar su ta dawowa daga ɗaurin auren da suka je Sokoto.
Ya bayyana cewa ƴan kasuwar sun tafi ne a cikin mota ƙirar kwasta mai ɗaukar mutum 40 da kuma mota ƙirar bas mai ɗaukar mutum 18.
Ranar Dimokuradiyya: Muhimman Abubuwan Da Buhari Ya Fada
A cewarsa, an sace su ne da yammacin Asabar a tsakanin Tureta da Bakura bayan sun baro ɗaurin auren da suka je a garin Tambuwal.
BBC dai ta tuntuɓi rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara domin jin ƙarin bayani kan wannan lamari, amma ba a samu ji daga bakinsu ba.
Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.
