Politics
BAYAN RASHIN NASARA A ZABEN FIDDA GWANI,MOGHALU YA FICE DAGA APC
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu, ya fice daga jam’iyyar APC bayan rashin samun tikitin takara
Moghalu, a wata takarda da ya aike wa shugaban APC, ya ce rashin adalcin da aka yi a zaɓen fidda gwani ne ya sa ya ɗauki wannan matakin
Ɗan takarar ya sha kaye ne a hannun Dumebi Kachikwu, yayin zaɓen fitar da gwani da ya gudana a Abeokuta
A wata takarda da ya aike wa shugaban jam’iyyar APC, Okey Nwosu, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya ce rashin adalcin da aka tafka a zaɓen fidda gwani ya sa ya bar APC.
Daily Trust ta ruwaito cewa Moghalu na ganin an tafka rashin adalci a zaɓen duk kuwa da matakan da jam’iyya ta yi iƙirarin ɗauka don aiwatar da sahihin zaɓe.
Bayan kusan mako daya da shan ƙasa a zaben fidda gwani, Tsohon gwamna ya tura wa Tinubu sako kan zaɓen 2023
Wani sashin takardar murabus din ya ce:
“Na rubuta wannan takarda ne domin miƙa murabus ɗina daga jam’iyyar ADC nan take. Na yi haka ne saboda zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa da ya gudana a Abekuta ya nuna cin karo tsakani na da jam’iyya.”
“Duk da jadawalin da kuka fitar kwanaki kaɗan kafin zabe wanda ya bayyana cewa jam’iyya zata ɗauki nauyin zuwa da wurin zaman Deleget a Abeokuta, wanda muka yi amanna kowane ɗan takara zai samu dama, APC ƙarƙashinka ta gaza cika haka.”
“Gazawar ku wanda ya nuna ƙarara cewa da gangan ne, ya haddasa kace-nace da magana mara daɗi kan matakan da aka bi na yin zaɓen, wanda ya haɗa da ɗauke Deleget da ba su cin hanci.”
Ɗan takarar ya ƙara da cewa wasu yan takara ciki har da shi kansa, sun ba da gudummuwar kuɗi ga asusun jam’iyya don ɗaukar nauyin deleget, amma komai ya canza.
Yayin da wanda ya samu nasara, Dumebi Kachikwu, ke da ƙuri’u 977, Moghalu ya samu kuri’u 589 a zaɓen.
