Politics
Yakamata APC Ta Baiwa Arewa Mason Gabas Mukamin Mataimakin Shugaban Kasa Domin Kada Atiku A Zabe—– Matasan APC
Daga Muslim yunus Abdullah
Kungiyar matasa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a shiyyar arewa maso gabas ta yi kira ga jam’iyyar APC da ta Mika mataimakin shugaban kasa ga yankin.
Darwin Nunez: Liverpool ta kulla yarjejeniya da Benfica kan dan kasar Uruguay
Shugaban kungiyar, Haruna Sardauna ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a Abuja.
Kungiyar ta yi nuni da cewa, maida matsayin yankin Arewa maso gabas zai kawar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya fito daga yankin.
Ta ce, “Mika mataimakin shugaban kasa zuwa Arewa maso Gabas zai kawar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP tare da samar da gagarumin goyon baya daga yankin da sauran shiyyoyin domin tabbatar da nasarar Alhaji Ahmed Bola Tinubu.
Kungiyar ta yi nuni da cewa duk wanda aka zaba daga yankin, musulmi ne ko Kirista zai tallafa musu.
Ya kara da cewa shiyyar Arewa maso gabas ta kasance tana baiwa jam’iyyar APC kuri’u tare da goyon bayan ‘yan takara daga yankin tun daga farko.
Kungiyar ta dage cewa ya kamata a duba yankin Arewa maso Gabas duba da irin sadaukarwar da yankin ya yi wa jam’iyyar ta APC Mai mulki.
