Connect with us

News

Joe Biden zai kai ziyara Saudiyya da Isra’ila .

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

Shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Gabas ta Tsakiya a karon farko a matsayinsa na shugaban ƙasa.

Matsalolin Nijeriya: Gyaran kundin tsarin mulki ne kawai mafita — Kawu Sumaila

Advertisement

Ana sa ran shugaban zai kai ziyara ƙasashen Saudiyya da Isra’ila da kuma wasu yankunan Palestine.

 

Shugaban zai yi tafiyar ne a watan Yuli mai zuwa inda zai shafe kwana huɗu yana rangadi.

 

Mista Biden dai zai kafa tarihi a matsayinsa na Shugaban Amurka idan ya je Saudiyya daga Isra’ila – hanya ce ta jirgi da Saudiyya ba ta cika bari ana bi ba sakamakon rashin jituwa irin ta diflomasiyya tsakanin Isra’ila da Saudiyya.

 

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending