Connect with us

News

SOJOJIN FARANSA SUN CAFKE KWAMANDAN IS A SAHEL

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

 

 

Sojojin Faransa a Mali sun cafke kwamandan Kungiyar IS reshen kasashen yankin Sahel kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar.

Ingila ta sha kashi mafi muni cikin shekaru 100

Advertisement

 

Sanarwar da rundunar sojin Faransa ta sanar ta ce, a tsakanin daren 11 zuwa 12 ga watan Yuni da muke ciki, rundunar Barkhane ta cafke Oumeya Ould Albakaye, jigo a kungiyar ta IS a kasashen da ke yankin kudu da Sahara.

 

Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin na Faransa ke shirin kammala janyewa baki daya daga Mali bayan sun shafe kusan shekaru 10 suna yaki da ayyukan ta’addanci a kasar.

 

Sojojin na Faransa sun dauki makwanni suna kitsa yadda za su kama kwamandan na IS akan iyakar Mali da Nijar.

Advertisement

 

Yanzu haka sojojin na Faransa za su yi wa Albakaye tambayoyi na tsawon kwanaki kafin daga bisani su mika shi ga hukumomin Mali don ci gaba da fuskantar tuhuma.

 

Wata majiyar tsaro da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, kiris ya rage ga Albakaye ya gaji kujerar tsohon shugaban IS a Sahel, wato Adnan Abu Walid al-Sahrawi wanda sojojin Faransa suka kashe shi a cikin watan Agustan bara.

 

Ana zargin Albakaye da cin zarafin fararen hula a kasashen Mali da Burkina Faso.

Advertisement

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending